|
|
|
|
A, uzu billahi minash shaidanir rajeem bismillahir rahamanir raheem, wasallallahu ala muhammadin wa alihid dayybinad dahireen.
Muna fa ida ta hudu, daga cikin fa idodin darussan al, milal wannihal, wadanda muka assa sasu domin yin bincike akan aqidun shi a, fa ida ta hudu itdace cewa zaiyuwu albarkacin wadannan darussan mutum ya fahimci cewa yan shi a, musulmine, kuma zai iya yuwuwa ya wuce haka, har ya fahinci cewa yan shi a, sune suke akan addinin musulunci na asali wadda ALLAH {T} ya aiko manzon shi alaihi afdalu salawatil musallin dashi
Muna bincikene akan wadan da mu awuya dan abi sufyan ya kashe munzo kan al imam hasan {as} kuma munyi bayani taqaitacce, kuma munyi bayanin yadda ya kashe shidin. Daga nanne kuma sai mukaga ya dace muyi bincike akan wata shubha.da ake gan gararwa akan al, imam hasan {as} da sauran dukkan a imma {as}da sauran salihan bayin allah da waliyai da ausiya da annabawan ALLAH {T}
Wannan tana da dangan taka da sanin gaibu, Inda suke cewa in dagaskene yasan gaibu, yaya akayi ya auri ita ja adah din? wadda ta sanya mashi guba? Sannan kuma yaya akayi yasha guba din har ya zama ta kashe shi?
Toوin munkoma kan inda muka tsaya amakon daya wuce, muna cewa ayoyin da sukayi Magana akan gaibi acikin al qur ani sun kasu kamar kashi biyu,muhimmai.
Kashi na farko yana cewa bawanda yasan gaibu, sai ALLAH
Sannan kashi na biyu, wadda shine muke akan shi yanzu, suna cewa wanin ALLAH yana iya sanin gaibu, amma da sharadi, da dalili da hikma,da wata maslaha daga ALLAH shi wannan din yake iya sanin gaibu din.
Muna kan wannan ayar inda ALLAH yake cewa. عَالِمُ الْغَيْبِ فَلَا يُظْهِرُ عَلَى غَيْبِهِ أَحَدًا (26) إِلَّا مَنِ ارْتَضَى مِنْ رَسُولٍ فَإِنَّهُ يَسْلُكُ مِنْ بَيْنِ يَدَيْهِ وَمِنْ خَلْفِهِ رَصَدًا
Wato cewa shi masanin gaibu shine ALLAH {T} kuma baya baiyanar da gaibun shi ga kowa,sai wanda ya yarda dashi daga manzanni,
To anan din a,wancan jilisan baya mun fara kawo tafsirin AL qurdabi,inda yake cewa ALLAH {T} bayan yayi nuni akan cewa babu wanda yasan gaibu inba shiba: to bayan ya fadi haka sai ALLAH ya toge,wanda ya yarda dashi daga manzannin.yace sai dashi kawai.
Kuma mukace wannan togo din yana daga cikin sharudda. dolele yazama cewa ALLAH ya yarda dashi kafin ya sami wannan matsayin.
To su wadannan zababbu daga cikin manzanni din, sai yazama ALLAH ya sanya gaibu daga cikinsu, saboda, ba dukansu ne yake basu ba.
Yana zabane daga cikin wadan da yagadama, sai ya sanar dashi ta hanyar wahayi,
Sannan sai ALLAH ya sanya wannan sanin da sukaima gaibi ya zama mu ujiza garesu.sannan kuma ya zama hujja ta gaskiya akan da awan da sukeyi akan cewa su annabawane.
Wannan kuma zaka sameshi acikin,al jami u lil ahkam fi ahkamul qur an, na al qurdabi, na abu Abdullah muhamd bn ahmad al ansary al qurdabi. Wanda ya rasu shekara 671 a darul riya I, turasil arabi bairut 1967 a nomban bugun, a juzu I na 19 shafi na 28.
Anan wurin qurdubi yatafi akan cewa wanin ALLAH yana iya sanin gaibu,mu samman muce annabawa,
Sannan bn ashu attunusi, yana cewa tunda ALLAH ya jingina siffan al,ilm izuwa ga gaibu,
Inda yace; alimul gaibu,ya {idafta } ya jingina siffan I,lim zuwa ga gaibu. Wanda yake kuma gaibu din masdar ne,
ALLAH baice {alimul gaib,ba.} sai ya zabi yayi amfani da masdarin ita kalma din,
To sai bn ashur yace wannan tarkibin da ALLAH yayi, inda yace عَالِمُ الْغَيْبِ
ALLAH ya, adafta masani izuwa ga gaibu. Yace wannan yana nufin kenan sanin dukkan haqa iq, na gaibu wadan da suke babu togo,
Lokacin da ALLAH yace {ALIMUL GAIBI} bawai {ALIMUL GA IB} yace ba.
Bn ashur Yace, alokacin da ALLAH yace, shi masanin gaibu ne, to abin da yake nufi, shine cewa babu wani jinsi daga cikin jinsosin gaibi wanda ALLAH bai sanshi ba.
Saboda haka alokacin da ALLAH yace عَالِمُ الْغَيْبِ to abin da yake nufi shine cewa babu wani nau I, na gaibu wadda bai sanshi ba.
Saboda haka dukkan masa,nif din gaibu ALLAH masanin sune. Kuma wanne nau in {mahiyoyine} ko dai daikun su, face ALLAH yasan su.
To daga nan bn ashur ya fara sharhi inda yake cewa wannan ya hada harda ma ana ta Kalmar gaibu.misalin ilimin ALLAH da zatinshi da siffofin shi.dukka ALLAH yasan wannan.
Shi ALLAH yasan zatin shi, zatin nashi a halarce yake gareshi da dukkan siffofin shi gabaki daya
Wannan kuma shine bayanin jinsi daya kenan na gaibu.wanda kuma mu bamu sani wannan ba.
Sannan ilimin ALLAH na gaibi ya hada harda al amuran da suke fakakku akan kansu, kamar misalin mala iku. Da al jannu. Wannan kuma shine na biyu.
Sannan ALLAH ya hada harda kwayoyin zarra,na abubuwan da idanu basu ganinsu, kamar abubuwan da zasu faru agaba,shi ALLAH yasan su.wadan da kuma shi ALLAH din wani lokaci yakan bada labarin cewa zasu faru, wasu kuma bai bada labarin su.
Saboda haka zabin da ALLAH yayi anan wurin alokacin da yayi amfani da Kalmar}GAIBI} abisa sigan masdar. To fifita wannan zabin na {MASDAR} acikin wannan ayan, yafi tattarowa awurin nuna fai fayewan ilimin ALLAH {T} ga dukkan wannan.
Wannan kuma gefe daya kenan.
Da ma anar cewa wayasan dukkan gaibu? Inba ALLAH ba? Inji bn ashur.
Ib ashur yaci gaba yana cewa, daga nan kuma sai ALLAH yayi {tafri i} ya dora akan wannan, yayi istis na I, yayi togo,
To alokacin da ALLAH yayi {tafri I,} yace عَالِمُ الْغَيْبِ
saboda shi kadai ne masanin gaibi, to sai yace, فَلَا يُظْهِرُ عَلَى غَيْبِهِ أَحَدًا Saboda haka baya baiyanar da gaibun shi ga kowa. Saboda shine alimul gaibu.
Ma anar wannan shine cewa shi ALLAH baya tsokaci kuma baya iddila antarwa,kuma baya bada labarin gaibu din,
Saboda haka inka lura da wannan to, yin amfani da Kalmar YUZHIRI yafi qarfi a, ma ana, akan yin amfani da Kalmar yudli u,
Wannan kuma yayine domin ka gane cewa kwata kwata ba wanda yasan ilimin gaubu sai ALLAH {T}
Domin inka lura shi Kalmar {YUZHIRU} yazone daga {AZZUHUUR} wato bayyana, wato mushahada.
Wato shi ALLAH baya shedarma kowa.
Kuma wannan yafi akan kace baya sa kowa yayi tsokaci,domin shi {YUZHIRU} ya hada harda ma anar {YUDLI U} din.
Shiyasama shi fi ilin aka,sashi yayi ta addi,akan alah, sai akace فَلَا يُظْهِرُ عَلَى غَيْبِهِ أَحَدًا
Kamar yadda yake cewa, {WAMA KANALLAHU LIYUDI AKUM ALAL GAIBI}
Saboda Kalmar yuzhiru, takunshi Kalmar yudli u, shiyasa ya zama fi ilin yayi ta addi, {ALAH} kamar dai {YUDLI U} din.
Wannan daya kenan.
Daga nan kuma sai yaci gaba yana Magana,yana newa afkuwan {fi ilin} acikin da irar korewa, tana nufin tattarowa gabaki daya ne,
Saboda wannan fi ilin da yake cewa {YUZHIRU} to afkuwan wannan fi ilin acikin da irar korewa baya baiyanarwa, wato ma anar shi shine cewa kwata kwata ALLAH baya baiyanar da gaibun shi.
Wannan daya kenan.
To hakama afkuwan maf ulin fi ilin {YUZHIRI } yake,al halin kuma yazo a, {nakra}, cewa {AHDAN} acikin HAIYIZIN NAHYU}
To alokacin da yazama cewa maf ul, din yuzhiru, na farko yazo a {nakra}, sannan nabiyu shima yazo a kar kashin rumfar korewa, to wannan shima yana nufin u,mum ne.
Wato kenan tunda shi ALLAH shine alimul gaibi,saboda haka baya baiyanarwa kowa da gaibin shi, mud,laqan umuman,babu qaidi, wannan shine ma anr bangare na farko na ita ayar,
Yaci gaba sai yace bayan haka ne sai ALLAH yayi togo yayi istisna I, inji bn ashur attunusi.
Yace; ALLAH ya toge wanda ya yarda dashi bayan ya kore dukkan kowa, daga gaibu,sai ya fitar da wanda ya yarda dashi
Wato sabanin wanda ALLAH ya ya yarda dashi, dukkn sauran nau o I,na mutane wadan da ALLAH bai yarda dasuba,, su zasu shiga cikin hukuncin umum ne.
Saboda haka duk abin da yafita daga cikin da irar togo, to zai shiga cikin hukuncin umum ne. saboda haka sanin gaibu, sai wanda ALLAH ya yarda dashi.
Saboda haka sai wanda ALLAH ya kebe, sai ya sashi ya zama yana iya sanin wani sahi na gaibi, ba wai duka ba. Saboda bawan da yake da hanya I,zuwa ga sanin zatin ALLAH . saboda shima misdaq ne, daga cikin masadiq din gaibu.
Saboda haka gaibun da ALLAH yaso ya baiyanar dashi ,daga jam in gaibu. To sai ya baiyanar ma irin wadan nan wadan da yaso din. Kamar yadda yake yin wahayi, saboda ai, shi wahayi yana daga cikin gaibun ALLAH {T}
To hakama duk abin da ALLAH yaso ya qarfafa manzon shi dashi,ta hanyar qarfafawa tak winiya,ya aiyada shi, ya kimsa mashi,ya aiyanashi kamar manzo {saw} to sai,,ya sanar dashi ya nuna mashi shi din.
Wannan din kuma na daga bada labarai ne, banda al qur ani,zai zama cewa ALLAH yana bashi labarai, na abin da zai afku agaba,kokuma ya sanar dashi abin dake cikin zukata aboye,
Saboda haka wannan fadin ALLAH {T} din cewa {IRTADAH} wato ya yarda dashi; to wannan din kebewane daga {AHDAN}
Wato {FALA YUZHIRI ALA GAIBIHI AHDAN, ILLA MANURTADAH} wato daga cikin {AHDAN } din. Sai wanda ALLAH ya yarda dashi,
Saboda haka {IRTADAH} istisna I, ne daga {AHDAN} wato in aka tambayeka akance wanene mustas na I,minhu? Sai kace {AHDAN}
Wannan shine abin da ake kwatan tawa, cewa {ILLAH MANIR TADAHU} saboda haka shi ALLAH shine masanin gaibu, wadda kuma baya baiyanar da gaibun shi ga kowa, sai wanda ya yarda dashi.
Saboda haka sai wanda ALLAH ya zabe shi domin yayi tsokaci zuwa gareshi ga gaibu, domin wata hikma wadda ALLAH yaso.
Wannan kuma shine abin da bn ashur ya fadi acikin tafsirin shi, mai suna attahrir wadda akafi sanin shi da tafsirin bn ashur.
Kuma zaka,sami wannan bayanin a sabon bugun shi, a dab a, ta farko na shekara ta 1420, juzu I na 29, shafi na 230.
To inka fahimci cewa ALLAH {T} awani wuri a, alqur ani yace shi kadai yasan gaibu, sannan awasu wurare kuma acikin alqur ani din yace wasu bashiba suna sanin gaibu din, amma da wasu sharudda, da qa ida, da hikma.
To inka fahimci wannan, to sai muzo muce, a, inane a alqur ani ALLAH yace wasu bayan shi suma sun san gaibu din?
To anan ma akwai ayoyi masu yawa acikin AL QUR ANI, amma bamu da lokacin kawosu, saboda bashine bahasinmu na asaliba, amma bari mubaka misalin wasu daga ciki.
Aacikin suratil fathi, ALLAH {T} yana cewa
لَقَدْ صَدَقَ اللَّهُ رَسُولَهُ الرُّؤْيَا بِالْحَقِّ لَتَدْخُلُنَّ الْمَسْجِدَ الْحَرَامَ إِنْ شَاءَ اللَّهُ آمِنِينَ مُحَلِّقِينَ رُءُوسَكُمْ وَمُقَصِّرِينَ لَا تَخَافُونَ فَعَلِمَ مَا لَمْ تَعْلَمُوا فَجَعَلَ مِنْ دُونِ ذَلِكَ فَتْحًا قَرِيبًا
Wato hakika ALLAH ya gasgatama manzon shi, mafarkin da yayi nagaskiya,
Kaga anan wurin ALLAH ya sanar da manzon shine ta hanyar arru uya sadiqah.
Yazama cewa shi manzon yasan abin da mutane basu saniba. Kuma wannan qad an zai afku.
To menene wannan mafarkin da manzon yayi, wadda ALLAH ya gasgata mashi?
Shine cewa lallai tabbas sai kunshiga masallaci mai,al farma insha allahu kuma kuna masu aske sumanku,gabakidaya, kuna masu saisaye, batare da kunajin tsoroba.
Anan ALLAH yaba da labari ya gayama manzon shi acikin mafarki ya nuna mashi abinda zai faru anan gaba,cewa tabbas tabbas zasu shiga masjidul haram. Sannan yasan abin da ku baku saniba.
Wannan daya kenan.
Nabiyu kuma shine cewa zamu kawo labarin wanda ba annabi bane amma kuma ALLAH ya sanar dashi gaibi.
Acikin AL QYR ANI ALLAH yana cewa
وَأَوْحَيْنَا إِلَى أُمِّ مُوسَى أَنْ أَرْضِعِيهِ فَإِذَا خِفْتِ عَلَيْهِ فَأَلْقِيهِ فِي الْيَمِّ وَلَا تَخَافِي وَلَا تَحْزَنِي إِنَّا رَادُّوهُ إِلَيْكِ وَجَاعِلُوهُ مِنَ الْمُرْسَلِينَ (7)
Wato munyi wahayi zuwa ga mahaifiyar musa akan cewa shayar dashi,
Cewa mu mukai mata wahayi akan cewa ta shayar dashi,
ALLAH yaci gaba yana cewa {FA IZA KIFTU ALAIHI FA ALQIHI FILYAMMI,
Idan kikaji tsoro cewa wani abu zai sameshi, to kijefashi acikin ruwa,
Kuma in kin jefashi din,{WALA TAKAFI WALA TAHAZIN} kada kiji tsoro kuma kada kiyi baqinciki,kada kiji kunci acikin ranki.
{INNA RAADUHU ILAIKI, WAJA ILUHU MINAL MURSALEEN} zamu dawo dashi zuwa gareki, kuma zamu sanyan shi daga cikin manzanni.
Wannan zaka sameshi acikin suratil qasas.
Ita wannan ayan tayi nuni akan iddila in mahaifiyar musa akan gaibi,alhali kuma ita bata cikin annabawa kuma bata cikin ausiya din annabawan.
Wadda wannan yana nuni ne akan cewa wanda ba annabi ba ,kuma ba wasiyi bane yana iya sanin gaibi,kuma har ALLAH yayi Magana dashi ,kota hanyar mala ikah,
yin hakan kuma sunan shi wahayi, amma ba wahayin risalaba.
Wadda wannan kuma shine mutane suke samun shubuha dashi, yasa suke kore sanin gaibi ga kowa gabaki daya. Saboda shi gaibi masadiq dinshi suna da yawa.
Inda badon muna Magana akan mutane bane anan wurin,da sai muce har wanda ba mutum ba ALLAH {T } yayi mashi wahayi,
Bakaji ba inda ALLAH yake cewa {WA AUHA RABBUKA ILANNAHAL}
Saboda haka inda ace ba muna Magana akan mutane bane, dasai mukawo ababen da ALLAH {T} yayi masu wahayi, gabaki daya. Amma mu bahasin mu akan mutum ne.
Saboda haka wahayi ga mutane kala kala ne,
Amma irin wannan wahayin da ALLAH yayi ga mahaifiyar musa {as] shi wannan sunan shi ilham,wato kimsawa. Ita ankimsa mata wadan nan umurne umurne, ne,ta yadda zata iya fahimta cewa ga abin da ake nufi, kuma wannan din ya shir ya tar da ita, har,ta tafi ga abin da aka shir ya tar da ita zuwa gareshi din.
Wannan kuma ya haqqaqar mana da abin da muke bukata, kafin muzo bahasi akan wannan din.
Cewa ALLAH ya kimsama mahaifiyar musa {as] wannan shiryatar wa din, wadda wannan kuma yana nufin cewa ne mahaifiyar musa {as} tana da wani iddila I, na sanin gaibi.
Wanda wani nau I, na wahayi wadda akece mashi ilham yazo mata dashi.
Sannan ba laifi bane ya zama cewa mala ika yana yin Magana da mutum koda wannan mutum din ba annabi bane, kamar yadda yayi da wata, har yakece mata {A,TA AJABINA MIN AMRILLAH?} wannan maganar, mala ikune suke gayama wata. Suna tambayarta cewa ,kina mamakine daga al, amarin ALLAH?
Nanfa ka duba akan cewa {MUKADAB }din mubasharatan shine matar ibrahim {as} bawai cewa akai wa ibrahim {as} gayamata kazaba, a,a, ita da kanta ne mala iku sukai Magana da ita.
Babu wani abu acikin al qur ani dayayi nuni da cewa ba kai tsaye mala ikun sukai Magana da itaba. Babu.
Kai tsaye sukai Magana da ita, al hali kuma ita ba annabiya bace.
WASALLALLAHU ALA MUHAMMADIN WA ALIHID DAYYBINAD DAHIREEN.
|
|
|
|
|